azlyrics.biz
a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 #

ali jita - labari lyrics

Loading...

prince production
(prince production)

labarin duniya ne
ku saurara mutane
wata ran kasha zuma ne
wata ran kasha madaci

ya al′umma ku lura
manya har ma da yara
daga zuci mu daina zara
wasu alwashi suke ci

wata rana nasara ce
wata rana matsala ce
ai wanan ka’idace
mai hakuri zaiyi dace

wani nada kudi a boye
bai farga ba sun tsiyaye
duniya mai juye, juye
wani yawo yanzu be ce

haka allah ke nufinsa
wani bawa ne akosa
wani garri zaya lasa
wani ko kaji yake ci

wani inda ka tashi zai je
wani na cinikin gidaje
haka harkar duniya ce
sai allah ya amince

in yau kaine kakeyi
gobe k+ma ba kai bane ba
lamarin ba kai kake ba
nufin allahu rabba

ga wani nata yabon mutane
wani na zagin mutane
wani gulma yake a zaune
bai san me ake ba

duniya sufa ta ball ce
sam ba suffar kwantance
mai lissafi ya mance
dan ba allah bane ba

ga wani malam mai karatu
wani ko yazai ya saitu
wani boka mai rubutu
wani ko yayaita rawar k+matu

wani dukanci ya keyi
wani ko jima ya keyi
ai wani tuki ya keyi
wani k+ma boko ya keyi

ai wani noma ya keyi
wanan d+nki ya keyi
wani saida waya ya keyi
wani dillanci ya keyi

kai koma me kakeyi
duniya mai sa bulayi
a cikinta akwai barayi
da akwai yan ball na yayi

wata sai kaunar masoyi
wata ko bacci take yi
wata gulma kawai take yi
wata girki ma take yi

wasu suyi hali na kaza
in sunci su goge baki
wasu suyi hali na karnai
kullum haushi da baki

wasu ko ′ya’yan agwagi
sun zarce uwa da dauki
wani zaki ne ku lura
a taba shi ya dau mataki
wani kura ne nufin sa
kwata ya saka a baki

labarin duniya ne
kuji zancen nan mutane

duniya da akwai saraki
wasu na manyan mataki
da akwai ulama’u sosai
sanan da akwai musakai
da akwai k+ma alhazawa
matsayin a fadesu sun kai

labarin duniya
labarin duniya ne

labarin duniya
labarin duniya ne

duniya
labarin duniya ne

duniya
labarin duniya

labarin duniya ne



Random Lyrics

HOT LYRICS

Loading...