hamisu breaker - yar arewa lyrics
duk wanda yayi gamo da abin kauna bai son rabewa
indai kwa ya rabe nishadi nai yai tarwatsewa
sirrin farin ciki soyayya nee ba takurawa
maiso asoshi kanso babu abinda bazai iyaba
na durkusa akan gwiwa taa dan kuskure nayi
ki yafiya gareni dan kin kama mini har maganai
nemanki na karade kauye na koma birane
fito naganki muyi kallon kauna kinji yar arewa
sirrin dake cikin raina duka nee zan bayyanawa
so yayi tsistsigi na taka yayyi mini illatarwa
ni bani fasa yarda domin kin zama rayuwata
manta dake hakan bansan yauushene zan iyaba
kukan dani nake da kishirwa bata gusheba
duk da nasani rabuwa bata zamto mutuwa ba
amma ki shaida in bangankiba gida bazan komaba
dan babu lafia in bake nima bazan iyaba
dashen da kikka min wata ‘ya bazan so tayi girbi ba
nazo da lallama hauragiya bazan fara gwaji ba
garinmu yai shiru sam banajin koda tsuntsaye
ina zan bincika dan nasan ke bakya da kawaye
nazamma majjanun kanki ban shakkar kowaye
akan nemanki yau na kodewa zafin sawaye
bazana soki dan kyau ba ko dan surarki
sai dan halinki hakuri nasan yauma ni nakureki
to karki manta dama tausayi alkhairi nee
kimin ni affuwa ra’ayina kanki bazai canza ba
na tambaya gurare ance bakya abokin gaba
to karki kirkireta akaina ni bazan jure ba
cinkon fure ki karba sanya shi ‘yar baba
kina a zuciya abadan nima bazaki fice ba
kallo na ruduwa ya zamo ina yiwa mataye
sam basu burge hamisu ra’ayina dayya ‘yar arewa
Random Lyrics
- sab zada - time lyrics
- chrom777 - desperation station lyrics
- asen - welcome lyrics
- rea1ity - pop lyrics
- cherbugro - finaly together lyrics
- hiax - was du nicht liebst lyrics
- tora (@1toraa) - blessed lyrics
- spacey jane - haircut lyrics
- shys debiocci - i am black history lyrics
- krystal brimner - young lyrics